Shugaban kasar Botswana Seretse Khama Ian Khama, ya ce giyar mulki ce ke hana shuwagabanin Afirka, son barin kan karagar mulki, da hadamar tara abun duniya.
Shugaban ya bayana haka ne a wata hira da wakilin Muryar Amurka, na sashen turanci Peter Clottey.
Shugaban na Botswana, ya kara da cewa tun farko ya shawarci tsohon shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, da cewa lokaci yayi ya sauka daga kan karagar mulki amma bai karbi shawararsa ba.
Ya na mai cewa yana fatar ‘yan Zimbabwe zasu dora akan wanna nasarar da kasar ta samu inda suka nuna karfin dimokradiya da kuma shawartar jama’ar kasar akan bin tafarkin demokradiya wajen gudane gudanen harkokin su na yau da gobe.
Shugaba Khama Ian Khama, ya kara jaddada cewa Zimbabwe tanada abinda kasar ke bukata domin bunkasa arzikin kasar da fatan cewa sabon shugaban zai yi sauyin da zai sake jawo masu saka jari a kasar domin tattalin arzikin kasar ya bukasa.
Ya kuma shawarci shuwagabanin Afirka, dasu guje duk abinda zai kai kasashensu ga shiga tasko ko kuma ya gurgunta zaman lafiya a kasashen.
Facebook Forum