Kungiyar Arewa Citizen for Change data kunshi samari mabiya addinin Musulunci dana Kirista ta kai ziyara jihar Bauchi a kokarin da take yi na farfado da zamantakewa dake tsakanin addinai biyu tun zamanin kaka da kakani.
Kungiyar ta Arewa Citizen For Change ta ziyarci shugabanin addinan biyu domin fahimtar dasu irin abubuwan da kungiyar take kokarin cimawa.
Shugaban kungiyar Barrister Sadiq Ilela yace kungiyar, ta hada matasa na arewacin Nigeria domin ci gaban yankin arewa.
Ya kuma ce daga cikin dalilan da suka yi nazari da shi, da yasa suka kafa kungiyar, shine suna ganin matsalolin da suke damun arewacin Nigeria na rashin zaman lafiya da fahimtar juna da kuma rashin darajawa da mutunta addinin juna.
Shugaban kungiyar Kirista a arewa maso gabashin Nigeria, Reverend Shuaibu Bet ya yabawa kasancewar kungiyar a yanzu. Yace yana da muhimmanci Musumi da Kirista su gargadi matasa akan su gujewa yin kalamai na batunci, su gujewa shaye shaye, kuma kada su yarda ana amfani dasu a zama yan banga masu tada zaune tsaye