Tun lokacin da aka kaddamar da zaben gundumomi da na kananan hukumomi rigingimu suka fara kunno kai. Yanzu an kwashe kusan mako guda ana ta kaiwa an komowa tsakanin bangaren jihar Borno Ibrahim Kashim Shettima da na tsohon gwamnan jihar Sanata Ali Modu Sheriff da kuma bangaren Mutawali Kashim Imam daya daga cikin jigajigan sabuwar jam'iyyar PDP da suka shiga APC. Rigingimun sun ta'allaka ne akan yadda za'a raba mukamai a jihar. Wannan rigimar tana neman raba jam'iyyar sakamakon irin jayayyaya da ake samu.
An kwashe kusan kwanaki hudu ana gudanarda tarukan siri tsamanin bangarorin uku akan yadda za'a warware matsalar domin kowanensu yana gwada karfinsa. Kawo yanzu dai babu wani sakamako, wato kowa ya dage akan matsayinsa. Lamarin ya sa 'ya'yan jam'iyyar suna tayin korafe-korafe domin rashin sanin tabbas musamman ga wadanda suke son su tsaya takara.
Wadanda suka yanki takardar tsayawa zabe sun sa ido su ga abun da zai wakana duk da wasu sun yi ikirarin an riga an yi zabe ko.
Shugabannin uku dake cikin takaddamar sun yi kokarin raba mukaman tsakaninsu amma har yanzu babu jittuwa. Gwamna Shettima an bashi kaso 40 na mukaman. Shi kuma Modu Sheriff da Mutawali kaso talatin talatin amma gwamnan ya ki amincewa. Da alama dai dangantaka tsakanin Modu Sheriff da gwamnan ta tabarbare.
Ga rahoton Haruna Dauda Biyu.