Idan ba'a manta ba kungiyar ma'aikatan kananan hukumomi ta dade tana kuka kan abun da tace ya hana ruwa gudu a kananan hukumomin kasa Najeriya. Kungiyar tace gwamnoni na yiwa kananan hukumomi shishshigi a harkokin kashe kudadensu.
Shugaban kungiyar ma'aikatan kananan hukumomi kasa baki daya Ibrahim Khalil yace tun shekarar 1999 da aka fara dimokradiya suka gano akwai gibi akan tsarin kananan hukumomi. Yace shi mutumin karkara gwamnoni basu daukeshi komi ba.
To amma Alhaji Salisu Sale Indirawa kwamishanan kananan hukumomin jihar Jigawa ya musanta zargi da APC tayi da kuma fahimtar ma'aikatan kananan hukumomin ta kasa. Yace a jihar Jigawa shugabannin kananan hukumomi suna cin gashin kansu. Yace da kwamishanan kudi ya karbo kudin jijhar za'a ware na kananan hukumomi a aika masu cikin asusunsu kai tsaye. Da zarar an tura masu kudinsu to ya rage garesu su yi tunanin abun da jama'arsu ke so. Kowace shekara kananan hukumomi suna yin kasafin kudi akan bukatun jama'arsu.
Ga rahoton Mahmud Kwari.