Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rigima ta Barke a Majalisar Dokokin Jamhuriyar Niger


Tambarin Jamhuriyar Nijar
Tambarin Jamhuriyar Nijar

A Jamhuriyar Niger wata takaddama ta kunno kai a majalisar dokokin kasar lamarin da ya kaiga dake taron majalisar sau da dama.

An kwashe wajen kwanaki uku ana kai da kawowa a majalisar dokokin jamhuriyar Niger.

Batun sabunta kwamitin koli na majalisar dokokin ya haddasa takaddamar tsakanin 'yan majalisar. 'Yan majalisa na adawa da masu rinjaye sun sha sauya kalamu mafi muni a majalisar. Hakan ya kaiga dake zaman majalisar sau da dama sakamakon rigimar da ta barke tsakaninsu akan zaben mataimakin shugaban majalisar dokokin. 'Yan adawa suna da mambobi biyu daga cikin biyar na kwamitin kolin.

Bayan rudanin da majalisar ta shiga har na kwanaki uku masu rinjaye sun kira wani taron manema labaru. Ben Umar Muhammed wani dan majalisa kuma mataimaki na hudu na shugaban majalisar dokokin yace ba'a taba yi ba a Niger ko a duniya a ce dan adawa ya zama shugaban majalisa. Ba zata yiwu ba. Dalili ke nan da suka ce hakan bai cancanta ba. Dan adawa ya koma adawa masu rinjaye kuma su dora wanda suke so akan kujera.

Su ma 'yan bangaren adawa sun kira taron manema labaru inda suka shaidawa jama'a cewa matsalar ba a nan take ba. Suka ce idan masu rinjaye suna neman tsige shugaban majalisar dokoki Hanma Ahmadu ko a nasu bangaren akwai gyaran da ya kamata a yiwa tsarin mulkin kasar. Injisu akwai gyaran fuska da ya kamata a yiwa dokar da zata hukunta shugaban kasa idan ya taka dokokin kasa. Sale Hassan Ahmadu dan majalisar dokoki na jam'iyyar lumana Afirka, wato jam'iyyar shugaban majalisar dokoki Hanma Ahmadu yace doka bata bayyana yadda za'a yi da shugaban kasa ba idan ya taka dokar kasa.

'Yan adawa sun yadda an yi kuskure amma a duk bangarorin biyu. Domin haka sai a yiwa kundun tsarin gyarar fuska wanda zai bayyana irin hukuncin da za'a yiwa shugaban kasa idan har ya taka dokar kasa.

Ga rahoton Abdullahi Mamman Ahmadu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG