Shugaba Uhuru Kenyatta na kasar Kenya da mataimakinsa William Ruto suna fuskantar caje cajen aikatawa jama'a laifi a kotun kasa da kasa. Zarge zagen sun kunno kai ne daga rawar da ake zargin, sun taka a tarzomar bayan zaben shekara ta dubu biyu da bakwai data kashe fiye da mutane dubu daya da dari daya.
Jakadan Kenya a Majalisar Dinkin Duniya Macharia Kamau, yace ya kamata kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya yayi la'akari da barazanar matakan tsaro a Kenya, bayan hare haren ta'adancin watan satumba da aka kai cibiyar hada hadar kasuwancin daya kashe akalla mutane sittin da bakwai.
A wata hira da sashen Swahili yayi da Jakadan a jiya Laraba, Mr Kamau yace ya kamata shugaba Kenyatta da mataimakinsa su maida hankali wajen tinkarar barazanar tsaro a kasarsu.
Yanzu haka dai ana yiwa mataimakin shugaban Kenya William Ruta shari'a a Hague kasar Holland. Shi kuma shugaba Kenyatta an shirya a ranar sha biyu ga watan gobe na Nuwamba, idan Allah ya kaimu za'a fara yi masa shari'a.
Kwamitin sulhu na Majalisar Dinki Duniya bashi da ikon soke shari;ar da ake yi amma yana da ikon jinkirata yin shari'a har na tsawon watani goma sha biyu, da za'a iya sabunta duk shekara.