Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zangazangar Janye Tallafin Man Fetur A Sudan


 Shugaban Sudan Omar al-Bashir
Shugaban Sudan Omar al-Bashir

Mummunar zangazangar adawa da janye tallafin man fetur na yaduwa a Sudan

Zangazangar da ke dada tsanani game da shawarar da gwamnatin Sudan ta yanke ta janye tallafin man fetur ta yi sanadin mutuwar akalla mutane shida a Khartoun babban birnin kasar.

An kashe masu zanga-zangar ne jiya Laraba a yayin wata arangama da jami'an tsaro. 'Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa kan masu zanga-zangar da ke ta jifa da duwatsu bayan kuma sun katse hanyoyi sun kuma banka wa gine-gine wuta.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun yi ta kiraye kirayen a kawar da Shugaba Omar al-Bashir, wanda ya shugabanci Sudan tun bayan da ya kwace mulki a 1989.

An fara zanga-zangar ce tun ranar Litini bayan da gwamnati ta bayar da sanarwar shirinta na janye tallafin man fetur a wani yinkuri na ceto tattalin arzikin kasar. Ranar Lahadi, Shugaba Bashir ya ce adadin tallafin ya kai wani mataki da ke barazana ga tattalin arzikin Sudan.

Janye tallafin ya janyo karin farashin mai sosai. Wannan al'amarin dai ya fusatar da 'yan kasar, wadanda su ka bazu bisa kan tituna su na ta zanga-zanga. An kashe mutane akalla biyu a zanga-zamgar da aka yi a farkon wannan satin.

Sudan ta fara fadawa cikin matsalar mai ne bayan da Kudancin Sudan ta sami 'yancin kan ta a 2011. Sabuwar kasar ta tafi da rubu'i uku na arzikin man fetur din kasar Sudan.

Amurka dai ta yi kiran da a kwantar da hankali a jiya Laraba. Ofishin Jakadancin Amurka da ke Khartoun ta yi kiran bangarorin biyu da su bai tayar da hankula su kuma mutunta 'yancin mutane.
XS
SM
MD
LG