A yayin da kungiyar Tarayyar Tattalin Arziki ta Afirka ta Yamma, ECOWAS, ko CDEAO, ta karbi shawarar bullo da katin shaida irin na zamani domin amfani a tsakanin kasashen yankin, mutane da dama su na tofa albarkacin baki a kan wannan matakin.
Wani direban mota dan kasar Ghana dake jigilar mutane daga Lagos a Najeriya zuwa Accra Ghana, Ali Alhassan, wanda aka fi sani da sunan Ali Fadama, yace ga matafiya irinsu, katin shaidar zai fi amfani da tasiri a saboda zasu fi jimawa a kan takardun Fasfo wadanda su a koyaushe aka zo tsallaka kasa sai an buga musu hatimi, abinda zai sa su cika a cikin kankanin lokaci.
Haka kuma yace matafiya su na fuskantar cin zarafi idan suka zo tsallaka wata kasa da takardun fasfo a saboda sai sun biya kudin cin hanci a yawancin lokuta kafin a buga musu hatimi a kai.
Yace ana matukar wulakanta matafiya a dukkan kasashen yankin Afirka ta Yamma, tare da yin kira ga kungiyar da ta gaggauta aiwatar da wannan mataki nata.