Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Jihar Kano Za Ta Saurari Ra'ayin Jama'a Kan Gyare-gyare A Kundin Tsarin Mulki


Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso na jihar Kano
Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso na jihar Kano

Yau Majalisar Wakilan Dokokin jihar Kano ke zaman sauraron ra'ayin jama'a kan batun garanbawul ga kundin tsarin mulkin Nijeiya

Yau Talata wakilan Majalisar Dokokin jihar Kano zasu cigaba da tafka mahawara akan kudirin daftarin yiwa kundin tsarin mulkin najeriya kwaskwarima, a wani mataki na amincewa ko rashin amincewar majalisar dangane da gyare-gyaren da Majalisar Tarayyar Nijeriya ke tunanin yi wa Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya, a cewar wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari.

Mai Tsawatawa Masu Rinjaye a Majalisar Dokokin jihar Kano Hon. Abdullahi Iliyasu Yaryasa ya ce lallai kam za su gwada abin da ke ra’ayin jama’a, da kuma abin da ke cikin daftarin yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin kasa, idan daftarin ya saba da abin da ke ra’ayin jama’a to lashakka za a yi watsi da shi. Shi ma mai wakiltar Fage a Majalisar Dokokin ta Kano Hon Abdullahi Yusuf ya ce za su duba sosai su gani. Muddun su ka ga wani sabon abu, wanda bai cikin abubuwan da su ka amince da su tun farko, to allai kuwa za su yi watsi da su. Shi kuwa Hon. Shu’aibu Tambai Doka Dawa, mai wakiltar Rimin-Gado, Dawakin Tofa da kuma Tofa ya ce dama sun bi lungu-lungu suna ta tambayar ra’ain jama’a, bayan sun bayyana masu abin da sassan kundin tsarin mulkin kasar ke nufi, kuma jama’a sun bayyana ra’ayoyinsu, wadanda za a duba a gani ko har yanzu sun a cikin daftarin.

Wakilin na mu ya kuma ji ta bakin Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin jihar Kano Hon. Hamisu Ibrahim, wanda ya ce su dai sun san sun gabatar da abin da ke ra’ayin jama’a. Ya ce kafin kuma su gabatar da ra’ayin jama’a ga matakin tarayya, sai da aka yi taron Majalisun Dokokin jihohin Nijeriya da kuma na arewacin Nijeriya.

Yau Jihar Kano za ta Saurari Ra'ayin Jama'a Kan Gyare-gyare a Kundin Tsarin Mulki - 3'14"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG