Kwamatin sulhu da tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya la’anci matakan hare-haren da sojin Gwamnatin Syria ke kaiwa farar hula masu zanga-zangar kin jinin Gwamnati, da la’antar kuntatawa ‘yancin Bil Adama da Gwamnatin Bashar al-Assad keyi.
Wannan, shine karo na farko da shugaban Syria zai bada umarnin tura tankunan yaki da soja da mayakan sunkuru su mamaye birnin Hama.
Jawabin la’antar da ya fito daga bakin shugaban Kwamatin sulhun jiya laraba, yayi shine bayan jinkirin watanni ukun da aka yi kwamatin na yin shiru kan rikicin siyasar kasar Syria.
Kwamatin sulhun yayi kira ga duk wanda keda hannu a rikicin na Syria da suyi hattara, amma jawabin na kwamitin sulhun bai bayyana bukatar azawa Syria takunkumi ba, ba’a kuma nemi da a gurfanar da shugabannin Syria a gaban kotun kasa da kasa domin fuskantar wani hukunci ba, kamar yadda ‘yan adawar Syria suka nemi da Majalisar Dinkin Duniya tayi.