A Asiya kasuwannin sayar da hannayen jari sun cira a fara hada hadar yau jumma a, bayan da kasuwannin Amurka suka farfado har da cin riba jiya.
Kasuwar shunkun Japan da ake kira Nikkei ta yi sama da kamar rabin kashi daya cikin dari a bude kasuwar yau jumma a, hakan ya kauda hasarar da ta samu a hada hadar jiya Alhamis. Haka ma kasuwannin shunku a New Zealand da Australia sun nuna alamun riba yau jumma a.
Wan nan farfadowa ta biyo bayan da kasuwannin Amurka da turai suka cira sama sosai a hada hadar jiya jiya Alhamis, suka farfado daga mummunar faduwa da suka yi ranar laraba, ‘yan kasuwa sun sami kwarin guiwa daga rahoto day a kunshi bayanai da ba zata ba dangane yawan mutane da aka dauka aiki a Amurka a baya bayan nan.
Kasuwar hannayen jari ta Dow Jones ta yi sama da kamar kashi hudu cikin dari,bayan ta fadi da kashi biyar ranar laraba. Kasuwannin NASDAQ da S&P suma sun ci riba a hada-hadar jiya Alhamis.
Alkaluma sun nuna cewa manyan kasuwannin sayar da hannayen jari a a London da Paris da Frankfurt duk sun tashi da riba a hada- hadar jiya Ahamis.
Ahalin yanzu kuma, kasashen Faransa, Italy, Andlusiya ko Spain, da Belgium sun haramta gwanjon hannayen jari domin dai-daita al’amura a ksuwannin sayar da hannayen jari inda ake cinikin kan mai uwa da wabi, kan fargabar bashi da ya addabi kasashe dake turai.