A wajen taron 'yan kasuwar kasar Nijer sun koka da makotan kasashe da kuma jami'an kwastam
WASHINGTON, DC —
A jamahuriyar Nijer wakilan kasashe tara na kungiyar yaki da hamada a yankin Sahel ta C.I.L.S.S a takaice sun yi wani taron wuni daya a birnin Niamey domin duba hanyoyin shawo kan matsalolin shigi da fici da bunkasa huldar kasuwanci tsakanin kasashen tara da su ka hada da Burkina Faso, Capo-Verde, Gambia, Guinée-Bissau, Mali, Mauritania, Niger, Sénégal, da kuma Tchadi. Taron ya samu halartar jami’an tsaro da kungiyoyin fararen hula da kuma na ‘yan kasuwa. Daga Niamey babban birnin kasar jamahuriyar Nijer ga wakilin Sashen Hausa Abdoulaye Mamane Amadou da ci gaban labarin.