Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Saliyo Ta Ayyan Dokar Ta-Baci Sanadiyar Wani Hari A Babban Barikin Sojan Kasar


FILE PHOTO: Sierra Leone's President and ruling party candidate Julius Maada Bio speaks after casting his vote at the 2023 Sierra Leone general election
FILE PHOTO: Sierra Leone's President and ruling party candidate Julius Maada Bio speaks after casting his vote at the 2023 Sierra Leone general election

Shugaban kasar Saliyo Julius Maada Bio, ya ayyana dokar ta-baci a fadin kasar a yau Lahadi bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a babban barikin sojoji kuma mafi girma a babban birnin kasar Afirka ta Yamma, sannan suka mamaye wuraren da ake tsare da mutane ciki har da wani babban gidan yari.

Harin da ya haifar da fargabar rushewar doka da oda a daidai lokacin da ake ci gaba da samun karin juyin mulki a yankin.

Cibiyoyin tsare mutanen da suka hada da gidan yari na Pademba Road Prisons - da ke tsare da fursunoni sama da 2,000 - an kai harin ne a daidai lokacin da jami'an tsaro ke kokarin kwantar da hankula yayin da ake ci gaba da harbe-harbe a barikin soji na Wilberforce, a cewar ministan yada labarai Chernor Bah.

“An mamaye gidajen yari kana maharan sun yi awon gaba da wasu fursunoni yayin da wasu da dama kuma aka sake su,” in ji Bah. Ya kara da cewa jami'an tsaro sun yi nasarar korar maharan zuwa wajen birnin inda ake ci gaba da gwabza fada.

Tun da farko shugaban kasar Saliyo Julius Maada Bio ya ayyana dokar ta-baci a fadin kasar sakamakon hare-haren.

Kamfanin dillancin labaran Associated Press a babban birnin kasar ya ce har yanzu ana jin karar harbe-harbe a birnin sa'o'i kadan bayan da gwamnati ta baiwa mazauna birnin tabbacin samun kwanciyar hankali, ko da yake ba a san ko su waye ke da hannu a musayar wutar ba, haka kuma ba a tabbatar da cewa an kama wasu ba.

Kungiyar tattalin arziki na yankin yammacin Afirka ECOWAS - wacce Saliyo ke cikinta - ta bayyana lamarin a matsayin wani shiri na "samun makamai da kuma kawo cikas ga zaman lafiya da tsarin mulki" a kasar.

A ‘yan watannin da suka gabata kungiyar ta yi kokarin dakile karuwan juyin mulkin da ake yi a yammacin Afirka da tsakiyar Afirka, wanda sojoji suka yi nasarar kwace iko sau takwas tun daga shekarar 2020, wanda na baya bayan nan suka faru a Nijar da Gabon a bana.

Kungiyar ta ECOWAS ta sake nanata cewa ba zata lamunta da sauya gwamnati ba bisa ka’ida ba.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG