Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karancin Ruwan Sama A Nijar Ya Sa Wasu Manoma Koma Wa Hakar Zinari


Wurin Hakar Zinari
Wurin Hakar Zinari

Kashi 40 cikin 100 na Manoma a jihar Agadas da ke arewacin Jamhuriya Nijar sun kaurace wa gonakinsu, inda suka koma harkar neman zinari bayan da suka samu kansu a halin tsaka mai wuya sakamakon matsalar karancin ruwan sama da aka samu a bana.

Masana sun yi gargadin cewa rashin isasshen ruwan sama a Nijar a bana ka iya haifar da karancin abinci da hauhawar farashin kayayyaki a kasuwanni, sai dai gwamnatin kasar ta ce ta na daukar matakai domin magance matsalar.

A bana manoma a jihar Agadas da ke arewacin Nijar sun samu kansu a cikin hali na tsaka mai wuya sakamakon karancin ruwan sama da aka fuskanta, lamarin da ya tilasta kusan kashi 40 cikin 100 na manoma barin gonakinsu domin zuwa wuraren hako zinari.

Adam Efangal, shi ne magajin garin yankin Tabelot, ya ce rashin ruwan sama ya shafi harkokin noma, don haka akan tilas manoma suka koma neman zinari.

Babu wani yanki a jihar Agadas da ake aikin noma da ya tsira daga iftila'in, lamarin da ya sa manoman tafka asara mai yawa, inji Madugu Nuhu, mamba a majalisar manoman jihar Agadas.

A gefe guda kuma, manoma masu yawa na tattare da barazanar rasa amfanin gona sakamakon bullar kwarin da ke lalata amfanin gona, to sai dai tuni hukumomi suka dauki matakin yin feshin magani, a cewar Mahaman Mu’azu, wanda ke kula da manoma a jihar Agadas.

Domin tabbatar da ganin an samu mafita kan irin matsalolin da manoman suke fuskanta ya sa hukumomin mulkin soja a Nijar ke shirin daukar matakai domin inganta harkokin noma.

Masana dai na gargadin kan yadda matsalar ka iya haifar da karancin abinci da tashin farashi a kasuwanni Nijar da ma wasu kasashen Afrika ta yamma irinsu Benin, Senegal, da Ivory Coast, duba da cewa kasashen sun dogara da Nijar ne wajen shigar musu da kayan amfanin gona kamar albasa, alkama, da kuma dankalin turawa.

Saurari rahoton Hamid Mahmoud:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG