Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Niger Na Neman Taimakon Jirage Masu Sarrafa Kansu Daga Amurka


A yayinda rundunar hadin guiwar kasashen da ake kira G5 Sahel ta kaddamar da ayyukan sintiri a fagen fama, hukumomin janhuriyar Niger sun bukaci kasar Amurka ta fara amfani da jirage masu sarrafa kansu domin fatattakar ‘yan ta’adda akan iyakar kasar da Mali.

Wannan matakin na matsayin wani bangare na huldar dake tsakanin Amurka da Niger a fannin tsaro, bayan da wasu 'yan bindiga da ake hasashen sun tsallako daga kasar Mali, suka hallaka sojojin Amurka hudu da takwarorin aikinsu na Niger guda hudu a kauyen Tongo-Tongo.

Dan majalisa Hama Asa, shine shugaban kwamitin tsaro a majalisar dokokin Niger, ya ce akwai 'yan ta'adda boye a Niger kuma suna shirya yadda zasu kai kai hari, amma idan akwai taimakon jiragen dake sarrafa kansu da ake kira Drone da turanci, za a iya samun bayanan makircin da suke kitsawa kafin su kai ga aikata shi.

Shi ko Hamidu Sidi, na hadakar kungiyoyin Platform a Niger cewa yayi kada a yi tuya a manta da albasa. Ya ce ya kamata a ba sojojin Niger kayan aiki ko a kara masu saboda suma suna da hazaka sosai.

Fargaba akan irin kuskuren da na’urori ke tafkawa musamman irin wadanda ke sarrafa kansu na cikin abubuwan da ‘yan kasar ke shakku akai.

Tun bayan tabarbarewar tsaro a yankunan Tillaberi, Tahoua da Diffa, kasar Amurka ta kara daukar matakan karfafa tallafawa janhuriyar Niger, mafarin girke dakarun Amurka a yankin Agadez Kenan, kuma bayanai daga hukumomin kasar na cewa a wannan sansanin ne ake saran jibge jiragen masu sarrafa kansu da kasar ta Niger ta bukaci Amurka ta zo da su a matsayin wani sabon matakin farautar ‘yan ta’adda akan iyakar Mali.

Ga Karin ayani daga Sule Mumuni Barma a cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00

Facebook Forum

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG