Yayin da majalisar dinkin duniya ta maida hankali kan matsalolin mata musamma na karkara a wani sashe nata, inda take wakilta wasu daga cikin kugiyoyin dake karkashin ta yin hidimar bada tallafi da sauran abubuwa, ko matan karkara da ake yi don su sun san da majalisar dinkin duniyar da ma abubuwan da take yi.
A cikin ayyukan da takeyi Majalisar Dinkin Duniya ta kebe sashi na musamman dake kula da mata da yara kanana. Mafi yawan abubuwan da tafi maida hankali akai ya jibanci harkar kiwon lafiya, ilimi, tattalin arziki samar da tsaftattacen ruwansha ga al’umma musamman mata na karkara da yara kanana. Har ma ta kirkiro ranaku na musamman na matan. Kungiyoyin da ke karkashinta sun eke gudanar da ayyukan kai tallafi.
Wasu matan karkaru a jihar damagaran sun shaida cewa basu san labarin wannan ranakun ba kuma sun bayyana matsalolin su na ruwa abinci da likitoci da na ilimi.
Da yadda suke shan mutukar wahala wajen neman ruwa a rafi, sunce musamman da kudinsu ma basa samu. Hukumar da ke kula da alumma, mata da yara kanana a damagaran na bakin kokarinta wajen kula da matsalolin matan musamman na karkara wajen rarraba musu dabbobi, kayayyakin sana’a da dai sauransu.
Sai dai hukumar nada saurana aiki na ta wayar da kan matan karkara da sanin Majalisar Dinkin Duniya da irin ayyukan da takeyi, ita kuma Majalisar Dinkin Duniya tace kungiyoyi da gwamnatoci su cigaba da taimakawa matan.
Facebook Forum