Cibiyayar leken asiri ta kasar Koriya ta Kudu tace mai yiwuwa Koriya ta arewa tana shirin gudanar da wani gwajin makami mai linzami, ‘yan kwanaki kafin shugaban Amurka Donald Trump ya isa yankin dake fama da sabanin ra’ayi.
Jami’an leken asirin sun shaidawa ‘yan majalisa yau alhamis cewa, sun lura ana gudanar da ayyuka a cibiyar nazarin makaman nukiliya ta Koriya ta arewa dake Pyongyang babban birnin kasar.
Koriya ta arewa ta gudanar da jerin gwaje gwajen makaman nukiliya a cikin shekarun nan, tare da yin watsi da takunkumin kasa da kasa da aka kakaba mata. Jami’an cibiyar leken asirin sun bayyanawa ‘yan majalisar cewa, mai yiwuwa wurin da Koriya ta arewa take gwajin makaman ya sami mummunan lahani bayan gwajin makaminta na shida, wanda ya kasance mafi karfi da ta gwada ranar uku ga watan Satumba, kasancewa fashewar ta haifar da kananan girgizar kasar uku bayan gwajin.
Facebook Forum