Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Siyasar Burundi dake Gudun Hijira Na Tsoron Komawa Kasarsu


Sojojin Burundi suna rakiyar 'yan adawan Burundi da suka cafko daga kasar Dimokradiyar Congo
Sojojin Burundi suna rakiyar 'yan adawan Burundi da suka cafko daga kasar Dimokradiyar Congo

Duk da kiraye-kirayen da ake yi masu su koma kasarsu ta Burundi, 'yan siyasa daga kasar dake sansanin 'yan gudun hijra a kasashen dake makwaftaka da Burundin suna gudun ransu saboda wai shugaban kasar zai hallakasu idan sun koma

: ‘Yan siyasar Burundi da ke gudun hijira sun ce za su fada cikin hadari muddun su ka tafi gida, duk kuwa da kiraye-kirayen da shugabanni ke yi a kasar ta Burundi da sauran kasashen yankin tsakiyar Afirka cewa su bar sansanonin su koma kasashensu.

‘Yangudun hijirar da su ka yi magana da Muryar Amurka, sun ce suna tsoron bita-da-kullin gwamnati muddun su ka koma Burundi, inda Shugaba Pierre Nkurunziza ya cigaba da kasancewa Shugaban kasa, bayan ya yi biris da kin amincewar da aka nuna a cikin kasar da kuma waje, game da yinkurinsa na nemar wa’adi na uku a 2015.

Dambarwar siyasa da kuma tashe-tashen hankulan da wannan shawarar da Shugaban kasar ya yanke ta janyo, sun sa ‘yan Burundi wajen 400,000 gudu zuwa makwabtan kasashe, musamman Rwanda da Uganda da kuma Tanzaniya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG