Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar Za Ta Fara Aikin Samar Da Wutar Lantarki Mai Amfani Da Makamashin Iska


Wutar lantarki
Wutar lantarki

Wata kungiyar kasar Birtanniya mai suna Savannah Energies ce, mai kokarin samarwa kasashen Afirka wutar lantarki a farashi mai sauki ta soma aikin a garin Mekera na jihar Tahoua.

Kuma tuni hukumomin kasar suka isa wurin don neman kungiyar da ta gaggauta kamalla aikin da zai samarwa matasa aikin yi, da ba da damar girka masana'antu da dama, wannan ko biyo bayan daukar darasi da kasar ta ce ta yi bayan datse mata wuta da Najeriyav ta yi sanadiyyar juyin mulki a 2023

Biyo bayan hambare Bazum Mohamed daga kan karagar mulki ne, kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Africa ECOWAS/CEDEAO ta karkabawa Nijar takunkumai ciki ko har da cirewa kasar wutar lantarki daga Tarrayar Najeriya.

Kuma tun a wannan lokacin ne, 'yan kasar da hukumomin mulkin sojan kasar suka soma tunanin hanyoyin kaucewa sake fadawa wannan matsalar, abin da ya sa, wadansu 'yan kasar ta Nijar da wata kungiyar kasar Birtaniya mai suna Savannah Energie, suka soma aikin dasa turukan na'urori masu anfani da kadawar iska da zai baiwa kasar Megawatts 250 a garin Magaria Makera tsakanin gundumomin Malbaza da Madawa a cikin jihar Tahoua.

In za a tuna, ministan makamashin kasar Farfesa Amadu Haoua da rakiyar gwamnan jihar Tahoua suka garzaya a wurin don neman ganin kampanin ya gaugauta wannan aikin, tare da kamallawa a cikin lokaci.

Wannan aikin zai baiwa kasar damar samun kaifin wutar lantarkin da zai kai kashi 22 cikin 100 na bukatar kasar, yayin da za'a anfani da turuka 45 da zai ba da Jigawatts kusan 800 a kowace shekara.

Saurari cikakken rahoto daga:Harouna Mamane Bako:

Nijar Za Ta Fara Aikin Samar Da Wutar Lantarki Mai Amfani Da Makamashin Iska
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:06 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG