Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Japan Ana Kara Fargaba Wani Injin Makamashin Nukiliya Zai Yi Bindiga


Hayaki daga ciniyar Nukiliyar Japan,bayan mummunar girgizar-kasa da igiyar Tsunami da suka auka mata.
Hayaki daga ciniyar Nukiliyar Japan,bayan mummunar girgizar-kasa da igiyar Tsunami da suka auka mata.

Hukumar makamshin Nukiliya ta Japan ta ce ana fuskantar wani lamarin ko ta kwana a wani injin samar da makamashi ta nukiliyar kasar da girgizar kasa ta yi wa lahani.

Hukumar makamshin Nukiliya ta Japan ta ce ana fuskantar wani lamarin ko ta kwana a wani injin samar da makamashi ta nukiliyar kasar da girgizar kasa ta yi wa lahani.

Hukumar ta fada lahadi cewa, wata na’ura dake dai-daita zafin inji na uku a cibiyar Nukiliya dake Fukushima ya daina aiki,kuma kawai alamar zai yi bindiga,bayan inji na daya a cibiyar, ya yi bindiga jiya Asabar.

Wakilan Muriyar Amurka dake kusa da cibiyar sun fada yau lahadi cewa har yanzu ana ta samun huci,sa’o’I 24,bayan mummunar girgizar kasa mai karfin awo 8.9, da kuma igiyar ruwa, ko kuma tsunami,da suka aukawa kasar ranar jumma’a.

Hukumomin Japan sun umurci mazauna kusa da cibiyar su nisanci wurin kamar da kilomita 20,haka kuma ta fara rabawa mutane dake yankin kwayoyin maganin Iodine, domin garkuwa daga kamuwa da gubar daga sinadaran Nukiliya.

Zuwa yanzu rahotanni da ake samu sun nuna cewa fiyeda mutane dubu daya da dari uku ne suka mutu ko ba’a san inda suke ba,sakamnakon bala’o’in,Yansanda sunce girgizar da igiyar ruwan sun tilastawa mutane dubu metan da 15 neman matsguni.

Ahlin yanzu kuma a yayinda ake ci gaba da damuwa kan hadari da za’a iya fuskanta daga cibiyoyin nukiliyar Japan,sakamakon bala’o’I da suka aukawa kasar,dubban ‘yan kasar jamus ne suka yi zanga zanga nuna rashin amincewarsu da shirin gwamnatin kasar na fadada dogaro kan cibiyoyin Nukiliya a zaman wata kafar samar da makamshi.

XS
SM
MD
LG