Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gano Tururi Mai Guba A Tashar Nukuliyar Japan


Tashar Nukiliyar Japan da ke Fukushima.
Tashar Nukiliyar Japan da ke Fukushima.

Hukumomi a Japan sun ce yawan tururi mai guban da ke sacewa daga tashar makamin nukiliyar da girgizar kasa ta yi wa illa har wani sashenta ya kama da wuta ya fara yin barazana.

Hukumomi a Japan sun ce yawan tururi mai guban da ke sacewa daga tashar makamin nukiliyar da girgizar kasa ta yi wa illa har wani sashenta ya kama da wuta ya fara yin barazana.

A wani jawabinsa da aka yada ta gidajen talabijin a yau Talata, Firayim Minista Naoto Kan ya ce yawan tururi mai guban ya yi muni kuma inji shi akwai yiwuwar a sami karin sacewar tururi mai gubar. An gargadi tuk wanda ke zauna a inda bai wuce nisan kilomita 30 daga tashar Nukuliyar ta Fukushima ba da kar ya fita waje.

An gano karuwar tururi mai guba har a wuri mai nisa daga tashar irin birnin Tokyo, wajen kilomita 140 a bangaren Kudu, to amman hukumomi sun ce yawansa bai kai munzilin iya barazana ga lafiya ba.

A can kuma Arewa, masu ayyukan ceto na ta fama da baraguzan da su ka katse hanyoyi a kokarinsu na isa ga dubban mutanen da garuruwansu da kauyukansu su ka ruguje sanadiyyar girgizar kasar ta ran Jumma’a mai karfin 9 a ma’aunin girgizar kasa da kuma ambaliyar tsunami da ta biyo baya. Hukumomi sun ce an samo gawarwaki sama da 2,400 kuma har yanzu ba a san inda dubban mutane su ke ba.

An kawar da dukkannin ma’aikatan da basu muhimman sassan wannan tashar ta nukiliya kafin ma a kashe wutar kafin yamma ta yi a garin. Ma’aikata kalilan ne kawai aka bari a wurin don su yi ta kwarara ruwan teku kan tukwanen nukiliyar don hana karafunan murhun narkewa, wanda abin da zai biyo baya ba zai yi kyau ba.

A halin da ake ciki kuma kasuwar hada hadar hannun jarin Japan ta rikito a karo na biyu a yau Talata bayan da hukumomi su ka yi gargadin karuwar sacewar tururi mai guba daga tashar nukiliyar da girgizar kasa ta yi wa illa.

Masu saka hannun jarin da su ka kadu da lahanin da girgizar kasar da ambaliyar tsumanin das u ka afka wa kasar za su yi wa tattalin arzikinta, sun yi dari-darin day a sa hannayen jarin faduwa da 10% a yau Talata, wanda hakan na daya daga cikin mummunar faduwar kasuwar hannun jari a rana guda. Wannan ya biyo bayan ribibin sayar da hannayen jari na 6% a jiya Litini.

Sauran kasuwannin Asiya ma sun tafka asara.

XS
SM
MD
LG