Jami’ai a kasar Japan sun yi gargadi game da karuwar yoyon tururi mai guba a kewayen wata masana’antar samar da wutar lantarki ta nukiliya da ta lalace a sanadin girgizar kasa, ta kuma roki mutane dake zaune a yanki mai fadin kilomita talatin daga wannan masana’anta da su kulle kawunansu cikin gidaje kada su fita waje. A cikin wani jawabinsa da aka yada ta telebijin a fadin kasar yau talata, firayim minista Naoto Kan ya ce tururi mai guba ya bazu daga kundoji uku na sarrafa nukiliya a masana’antar nukiliya ta Fukushima bayan mummunar girgizar kasa ta ranar jumma’a, da mummunar igiyar ruwan tekun da ta biyo baya.
Mr. Kan yace wannan tururi mai guba yayi yawa, kuma har yanzu akwai barazanar karin yoyon irin wannan tururi mai guba. A yau talata da safe, an sake samun bindiga ta uku ta wani abu da ya fashe daga kundun injin nukiliya a masana’antar ta Fukushima, a bayan irin wannan bindiga a ranakun asabar da jiya litinin. Haka kuma jami’ai sun ce wuta ta kama a cikin kundu guda a wannan masana’antar nukiliya. Ba a bayar da rahoton mutuwar wani a cikin masana’antar ba. Wannan bala’in ya fara kunno kai a bayan da girgizar kasa da kuma igiyar ruwan telun da ta haddasa kazamiyar ambaliya suka janyo dauke wuta a ranar jumma’a, abinda ya nakkasa injunan dake fifita sandunan makamashi na nukiliya a cikin wannan kundu domin hana su narkewa. Jiya litinin, hukumar nazarin karkashin kasa ta Amurka ta sake duba na’urorinta ta ce girgizar kasar da aka yi a Japan ta kai awu tara ne daidai, ba ma awu takwas da digo tara da aka zata tun farko ba. An yi ta samun girgije-girgijen kasa a bayan ta farkon. Injiniyoyi su na ta kokarin famfon ruwan teku zuwa cikin kundojin dake masana’antar nukiliyar ta Fukushima domin sanyaya sandunan makamashin nukiliyar da nufin hana su yin zafin da zai sa su narke. Amma an ce ruwan yana taba wadannan sanduna masu dan karen zafi sai ya zamo tururi ya baje. Jami’an masana’antar sun ce an sanmu tururi mai guba da ya tsiyaye a wajen masana’antar.
An janye jiragen ruwa da na sama na mayakan Amurka na wani dan lokaci daga bakin gaba inda suek aikin bayarda agaji a saboda wannan tururi mai guba da aka ce ba ya da yawa sosai. An kwashe mutane kimanin dubu maitan daga yankunan dake kewaye da masana’antar ta Fukushima. Gwamnati ta shawarci wadanda ba su fice ba da su zauna cikin gidajensu kada su fita waje.