Kasar Ghana na tattaunawa da jami’an hukumar lamuni ta kasa-da-kasa wato IMF a turance, dangane da wani bashi da kasar take bukatar karba daga hukumar. A cewar Shugaban kasar ta Ghana John Dramani Mahama, taimako da kasar shi take nema da ga hukumar lamuni ta kasa-da-kasa zai taimaka matuka don ganin kasar tafita daga kalubalolin da take fuskanta, da kuma tai makawa wajen farfado da tattalin arzikin kasar. Amma kuma awani bangaren wannan mataki da shugaban yake son dauka yasha suka a wajen yan kasar, musamman ma ‘yan siyasa da ‘yan hamayya, sun kuma yi nuni da cewar karbar bashi daga wadannan hukumomin zai iya sa kasar cikin matsaloli da zai haifar da wasu cikas a kasar baki daya.
A ganin Alh. Halliru Kumasi wannan wani abu ne da bai dace ba, don koda an kar bo kudin to ba'a bun da za’ayi da su don cigaban 'yan kasa gana, ya kuma ce ai hukumar lamunin tana dari-dari da mulkin Ghana. Ya kuma ce ai kasar na da arzikin da bata bukatar bashin wata kasa ko hukuma.
A kuma wani bangare, wasu na ganin cewar hakan shine mafita ga kasar. A cewar wani tsohon dan jarida Usman Yahaya Aurad yace hakan yakamata don shugaban kasar zai samu damar da zai warkar da matsalolin kasar idan har ya karbo wannan bashin. Ya kuma yi nuni da cewar ‘yan siyasa su san yadda yakamat su dinga kushe abu ba kawai su dinga sa ra’ayin su a gaba ba kawai, su dinga mantawa da cigaban kasar baki daya.
Suma 'yan kasuwar kasar na ganin hakan yakamata idan har za'ayi amfani da kudin ta yadda yakamata.