Shugaban yayi fira da wakilin Muryar Amurka yayin da shugabannin kasashen Afirka suka yi taron koli da shugaba Obama na Amurka.
Cikin abubuwan da suka tattauna da shugaba Obama har da matsalar tsaro. Shugaban yace matakin farko da yakamata a dauka domin yin rigakafin harkokin tsaro shi na samun labari. Na biyu sun yi shawara akan taimakon da Amurka zata ba kasashen Afirka akan tsaro musamman domin horon sojojin nahiyar. Abu na uku da suka yi shawara da Amurka shi ne samun makaman da suka dace. Shugaba Obama ya amince kuma zai fara aiwatar da taimakon da kasashe shida, wato Niger, Najeriya, Ghana, Mali, Tunisia da Kenya domin ba kasashen daman karfafa tsaro.
Akan jiragen nan da basu da masu tukasu da Amurka ta jibge a kasar Niger shugaba Mahamadou Issoufou yace a cikin kasarsa bai fuskanci wani kalubale ba. Mutane basu yi suka ba, domin sun san anfanin Niger ne. Mutane sun san jiragen zasu ba gwamnantin kasar labari domin su dauki matakin rigakafi. Idan 'yan ta'ada zasu kawo hari suna da labari.
Dangane da abun da kungiyar Boko Haram keyi a Najeriya makwafciyar kasa, yace akwai matsalar tsaro da iyakar kasarsa. Misali a Libiya akwai tashin hankali. Mali ma haka. A Najeriya kuma bata canza zani ba. Akan matsalar Boko Haram a shekarar 2012 sun yi wani babban taro inda suka ce yakamata su hada karfinsu wajen neman labari da makamai domin a samu a ciwo kan matsalar.
Shugaba Mahamadou Issoufou baya zaton akwai 'yan Niger da yawa a cikin Boko Haram. Amma a Niger sun dauki karfafan matakai domin su kare iyakarsu da kare rayuwar 'yan Niger da dukiyarsu.
Ga karin bayani.