Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama, wanda kuma shine shugaban Kungiyar kasashen yamacin Afirka [ECOWAS] yace kai kawo na mutane da kayayyaki tsakanin kasashen yamacin Afirka,, da yin amfani da kudi bai daya da kuma katin sheda na ECOWAS da batun tsaro dakuma Ebola suna cikin mahimman abunda za’a yin mahauwara akai.
Ya bayana haka ne a lokaci da ake bude taron na kungiyar kasashen yamacin Afirka, a Accra, babban birnin kasar Ghana.
Ya kara da cewa kungiyar zata ci gaba da ba lamarin tsaro himma masamman a Najeriya , inda bom ya tashi a Abuja a kwanakin baya.
Kwamishiniyar, harkokin siyasa, tsaro da zaman lafiya ta kungiyar Salamatu, tace matakan da aka dauka a taron gaggawan da akayi akan yaki da ‘yan boko haram, da kuma na kasar Mali, zai kawo nasaran dakile ‘yan ta’addan.
Ta kara da cewa taron ya gano cewa wasu kasashen da bana yamacin Afirka ba yakamata a jawosu su shiga cikin maganar don suna kusa da najeriya kwarai.