Kabilun dake zaune a Zangon Accra Ghana duk sun halarci bikin da amsa gayyatar sarkin zuwa bikin nadinsa.
Shaikh Isma'il Abubakar mai lakabin ba mai yi sai Allah shi ne sarkin matasa na kabilar kwatakwali a birnin Accra kuma ya gargadi sarkin Hausawan da cewa ya mayar da hankali akan ilimin yara mata domin hausawa sun cika bada yara mata kanana aure lamarin dake hanasu yin karatu. Ilimi zai taimaka masu.
Sabon galadima da aka nada a wurin bikin Alhaji Usman Waikadiri Ingilish yayi kira ga hukumomin Najeriya da su kara himma wurin ceto yara mata sama da dari biyu da 'yan Boko Haram suka sace. Duk abun da ya taba Najeriya ya taba Ghana. Batun Boko Haram ya damesu kwarai. Yayi fatan Allah ya kiyaye ya kuma tona asirin wadanda suke da hannu a lamarin. Sauran shugabannin Afirka su ma su tashi su taimaki Najeriya.
A wurin bikin nadin sarkin an baje al'adu daban daban na Hausawa tare da kade kade irin na kasashen Hausa.
Wazirin birnin Kumasi Alhaji Dan Tsoho shi ma yana cikin taron. Ya gamsu da bikin kuma yace sai dai a yiwa Allah godiya. Ya kira a tanada al'adun Hausa domin an sha'afa.
Wasu mahalarta taron sun gargadi sarkin ya samu fadawa masu adalci domin ya gudanar da mulki da ya kayatar. Wasu kuma suna murnar cewa Hausawa basu manta da al'adunsu ba kuma suna fata zasu cigaba da karesu.
Ga rahoton Baba Yakubu Makeri.