A wajen taron bita na kwana biyu babban Hafsan Sojojin kasa Na Najeriya, Janar Tukur Buratai, ya ce samarwa da sojoji makamai zai ‘kara kaimin rundunar wajen ci gaba da tunkarar kalubalen tsaro dake ‘kara kunno kai da canza salo a Najeriya.
Taron na sojojin na zuwa ne kwana guda bayan da gwamnatin Najeriya ta ce ta kebe dalar Amurka Biliyan daya don sayawa sojojin makamai.
A cewar shugaban kwamitin sojojin na Majalisar wakilan Najeriya, Rimande Shawulu, ta’addanci abu ne dake daukan dogon lokaci kafin a gama da shi.
A baya dai an taba ware makudan kudade domin sayawa sojojin Najeriya makamai amma kuma aka wawure kudin. Tsohon gwamnan mulkin soja na jihar Kano, kanal Aminu Isah Kwantagora, ya ce bashi da fargabar za a iya sake maimaita abin da ya faru a baya na wawure kudaden makaman.
Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.
Facebook Forum