Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Bindiga da Dama a Zamfara


Gumurzun sojojin Najeriya da 'yan bindiga
Gumurzun sojojin Najeriya da 'yan bindiga

Da alamar kwalliya ta fara biyan kudin sabula dangane da tura sojoji zuwa jahar Zamfara da gwamnatin Najeriya ta yi, saboda tuni har sun hallaka 21 daga cikinsu a gumurzun farko.

‘Yan kwanaki da bayan da gwamnatin Najeriya ta tura sojoji zuwa jahar Zamfara saboda su tinkari miyagun nan da su ka kashe mutane da dama a jahar, an fafata inda sojojin su ka kashe da dama daga cikin miyagun. To amma su ma sojojin sun rasa biyu daga cikin baradensu.

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da aukuwar wannan arangamar a wata takardar sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in yada labaran Rundunar Sojin Najeriya Burgediya Texas Chukuwu, wadda ta ce an yi gumurzun ne a kauyen Tungar Daji da ke Karamar Hukumar Anka da ke jahar ta Zamfara, inda sojojin su ka aika da ‘yan bindiga akalla 21 zuwa lahira.

Sojojin, wadanda su ka kuma raunata da dama daga cikin ‘yan bindigar sun kwace makamai da dama na miyagun.

Ga wakilinmu Murtala Sanyinna da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG