Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Mahara Daga Jihar Filato Sun Kai Hari Taraba


 Gwamna Darius Dickson na jihar Taraba
Gwamna Darius Dickson na jihar Taraba

Rahotanni daga jihar Taraba na cewa wasu mahara daga jihar Filato sun kai wani hari a wasu yankuna na jihar Taraba arewa maso gabashin Najeriya inda aka samu asarar rayuka da sace dukiya bayan awon gaba da suka yi da wasu mazauna yankunan da aka kai harin, kuma kawo yanzu har an tura jami’an tsaro.

Rahotanni na cewa wasu mahara ne daga kauyukan jihar Filato suka ketaro tare da farma wasu kauyukan kananan hukumomin Karim Lamido da Ibbi na jihar Taraba inda har aka samu asarar rayuka, baya ga dukiyar da suka sace, haka kuma sun yi awon gaba da wasu mutane.

Mr. Naanmi Daniang, Dagacin Fumang, a karamar hukumar Karim Lamido da yanzu haka yake gudun hijira a Jalingo fadar jihar Taraba, ya bayyana yadda aka kai musu hari a Kanshar dawasu kauyuka na yankin.

Shima da yake Karin haske, Hon.Baba Muhammad Usman, kansila dake wakiltar mazabar Ammar, ya ce bai ga wadanda aka kashe ba har ila yau amma maharan sun sace wasu al’umman yankin sun yi awon gaba da su.

Shima wani ganau ya bayyana cewa ba wannan ne karon farko da maharan kan ketaro daga yankin jihar Filato zuwa Taraba don kai hari ba, duk kuwa da matakan da aka dauka a baya.

To sai dai kuma,da Muryar Amurka ta tuntubi daya daga cikin shugabanin al’umman Tarok dake makwabtaka da wadannan yankuna da aka kaiwa harin ya musanta zargin cewa suke kai harin sari-ka-noken.

Tuni aka tura karin jami’an tsaro zuwa yankin don kare rayuka. ASP David Misal shi ne kakakin rundunan ‘yan sandan jihar Taraban ya ce an dau mataki a yanzu.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:50 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG