Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ya ja kunnuwan iyaye da su guji cire 'ya'yansu mata daga makaranta da zummar aurar dasu tun suna 'yan kanana.
Gwamnan ya yi gargadin ne lokacin da yake jawabin bankwana a bikin yaye wasu dalibai 'ya'yan makiyaya dake samun karatu a makarantar El-Kanemi a cikin garin Maiduguri. Gwamnatin jihar Borno ce ta dauki nauyinsu.
Tun watanni bakwan da suka gabata gwamnatin ta dauki nauyin karatun 'ya'yan Fulanin su 35 da ake ba ilimin addini da na zamani a makarantar. Amma a cikin watannin suka kai 525 sakamakon tururuwan da Fulani keyi suna shogowa jihar.
Jiya Alhamis aka ba daliban hutu kuma Gwamnan ya sake rabawa iyayen yaran kayan abinci domin su ci gaba da ciyar da 'ya'yansu a gidajensu.
Gwamnan ya sake kiran iyaye da su guji aurar da 'ya'yansu da basu isa aure ba. Injishi duk wanda ya aurar da diyarsa 'yar shekaru goma ko sha biyar zasu shiga kafar wando daya da gwamnati.
Ya ce an koroku daga arewacin Borno kun zo nan kuna aikin gadi amma su sani nan da shekaru 20 ko aikin gadin ma ba za'a samu ba saboda haka wajibi n su bar 'ya'yansu su yi karatu saboda Fulani 'yan kasa ne.
Rahoton Haruna Dauda nada karin bayani
Facebook Forum