Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karin Haske Kan Batuttuwan Da Aka Tattauna A Taron Kungiyar Kasashen Afirka


Taron kungiyar tarayyar Afirka karo na 35 a Ethiopia
Taron kungiyar tarayyar Afirka karo na 35 a Ethiopia

Kungiyar tarayyar Afirka ta kammala taron ta na kwanaki biyu a hedikwatar birnin Addis Ababa dake kasar Ethiopia, tare da yanke muhimman shawarwari.

Kungiyar ta yanke wasu shawarwari ne akan juye-juyen mulki a Afirka ta Yamma da matsalolin tsaron da ya mamaye kasashe da dama.

Malam Garba Shehu kakaki a fadar gwamnatin Najeriya ya yi mana karin bayani bayan da shugaban kasar Buhari ya sauka a birnin tarayya Abuja.

Garba Shehu ya fara da cewa wannan karon, shugabannin sun hadu da juna ba kamar yadda da suka yi ba ta yanar gizo saboda yaduwar annobar coronavirus.

Ya ce sun tattauna akan batutuwa da dama musamman akan batun juye-juyen mulki da ke yawan fa faruwa yanzu a Afirka ta Yamma da kuma sha’anin rashin tsaro sakamakon hare-hauren ‘yan bindiga.

Ya kara da cewa shugaba Buhari ya yi magana akan tsaro da yadda ake kashe makudan kudi don yaki da rashin tsaro amma har yanzu da saura, kuma yayi magana akan taimakawa a wurare dabam-dabam a kara hadin kai da sauran kasashen.

Saurari rahoto cikin sauti daga Umar Farouk Musa daga Abuja:

Karin Haske Akan Batuttuwan Da Aka Tattauna A Taron Kungiyar Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG