Abokin aiki Bello Galadanchi ya zanta da wani ganao, mazauni a kasar Masar, Ahmed Abba Majidadi Binanchi. Lamarin sai kara rincabewa ya ke yi domin yau magoya bayan hambararen shugaba Morsi da na gwamnatin yanzu sun fito zanga zanga kana jami'an tsaro sun bazu koina. Magoya bayan Morsi suna Allahh ya isa domin, injisu, an kashe masu mutane fiye da dubu uku. Suna daga tuta suna cewa gwamnatin yanzu ta kau Morsi ya dawo kan karagar milki.
Harkokin yau da kullum sun tsaya cik domin yawacin shaguna a rufe suke. Motocin haya babu su idan kuma akwai sun ninka kudi ninkin baninkin. Hatta gidanjen mai an rufesu domin fashe-fashe da aka yi. Ma'aikatu sun dena aiki domin rashin tabbas.
Babu tunanin wannan rikici zai kawo karshe nan da 'yan kwanaki domin magoya bayan Morsi sun ce mutuwa ma suke so. Don haka ana kashesu suna kara fitowa. Kamar yadda wani masanin tarihin kasar ya fada da can 'yan Jam'iyyar 'Yan'uwa Musulmi sun saba da sadakar da ransu. Sun saba da aka kullesu da kuma muzguna masu a gwagwarmayarsu da tafi shekaru hamsin suna yi da gwamnatocin kasar. Don haka wannan ba shi ne farko ba kuma zasu jaje sai dai a cigaba da kashesu.
Ga karin rahoto.