Yau gwamnatin da take da daurin gindin sojojin kasar ta yi yunkurin kawar da mutanen ko ta halin yaya. Wanna yunkurin ya kaiga gumurzu tsakanin jami'an tsaro da masu zanga zanga lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da yawa wasu kuma da dama suka jikata.
Rahotannin dake fitowa daga kasar sun yi karo da juna. Domin sanin gaskiyar abubuwan dake faruwa abokiyar aiki Jummai Ali ta zanta da ganau dake birnin Alkahira. Mutum na farko da ya yi magana Malam Ahmed Abba Majidadi Binanchi ya ce birnin Alkahira sai dai addu'a domin harkoki sun rikice sai a godewa Allah. Kodayake lamarin bai shafi dalibai 'yan kasashen waje ba amma tsakanin 'yan kasar Ahmed ya ce an yi kashe kashe ba adadi. Ya ce ba zai iya bada adadin wadanda aka kashe ba to amma suna da yawa. Su kuma yanzu suna gida ba fita. Shaguna suna rufe. Babu abin dake tafiya na harkar rayuwa. Ya ce daga abubuwan da suke kallo a tashar Aljazeera suna ganin masu goyon bayan Morsi sai kara fiowa suke yi suna kiran Morsi ya dawo duk da kashesun da ake yi. Duk da wai an wargaza wuraren da suka kama amma sai cigaba da fitowa suke yi. Basa tsoron mutuwa. Wai sun riga sun ce su mutuwa suke so idan ba shugaban kasarsu ya dawo ba.
A nashi bayanin Malam Aliyu Mohammed Kano ya ce babu abun da ya lafa domin su masu zanga zangar duk da wai basu da makamai kuma ana kashesu amma sai kara fitowa suke yi kan tituna. Sai dai ya ce akwai manya manyan malamai da suka fito suna kwantar da hankalin masu zanga zanga domin ko za'a samu 'yar masalaha. An ce jami'an tsaro suna cigaba da kashe mutane babu kama hannun yaro.
Ga karin bayani.