Abokiyar aiki Jammai Ali ta zanta da Dr. Usman Bugaje masanin tarihi wanda ya san tarihin kasar Masar ya kuma san yadda harkoki ke gudana a kasar.
A bayaninsa ya ce Allah kadai ya san abun da zai faru amma kungiyar 'Yan'uwa Musulmai ba zata bar abun da take yi ba.Duk kashe-kashen da a ke yi mata ba zai canza matsayinta ba domin ta sha shiga irin wannan abun. Ya ce yakamata a ce ita kanta gwamnatin Masar ta ce ta sansu domin ba da fada ba ne da za'a iya kawo karshensa ko da karfin soji a wuraren da suka mamaye. A wannan gumurzun ma ana kashesu a wani wuri ana rushe asibitocin da suka bude domin su taimaki 'yanuwansu da suka jikata suna kuma dada fitowa babu fashi. Su mutuwa a wurinsu sun dade suna yi kuma bata hanasu yin gwagwarmaya. Kuskure ne gwamnatin kasar Masar ke yi da daukan wannan mataki na murkushesu da karfi da yaji. Ya kamata a ce kasashe kamar su Amurka sun hana gwamnatin yin abun da take yi domin tasirin abun da zai biyo baya.
A tuna su ne yau suke kare dimokradiya domin zabe suka ci wanda aka yi cikin lumana. Ta yaya za'a ce an hambaresu domin ana kin jinisu sabili da addinisu. Wannan abun zai yi tasiri ba a kasar Masar kadai ba har ma da sauran kasashen larabawa.Kamata yayi gwamnati ta guje ma hadarin da ka biyo baya.
Dangane da umurnin da Amurka ta baiwa gwamnati ta sako 'yan kungiyar jam'iyyar Morsi wadda ta yi watsi shi da kuma amincewar Sanato John McCain cewa juyin mulki aka yi, ya ce duk da haka Amurka da na linzamin da zata ja ta hana abubuwan dake faruwa. Sai dai a yi addu'a kada kasar ta bi sawun kasar Siriya domin su 'yan'uwa Musulmai babu abun da suke shakka. Babu kuma wanda zai iya canza masu ra'ayinsu domin ra'ayi ne wanda yake da tushe da tarihi da kuma tasiri a wurinsu. Abu ne na akida. Abu ne wanda sai an zauna dasu an tabbatar masu da wasu abubuwan da za'a yi. Wani abu da ka iya faruwa bayan yau da aka yi masu kisan kiyashi wadanda da basa sonsu ka iya basu goyon baya yanzu. Cikin wadanda aka kashe akwai mata. Sako Morsi koda ma za'a yi masa daurin talala da sauran manyansu shi ne mafita.
Ga karin bayani.