A Jamhuriyar Nijar kwamitin yaki da illolin da ke da nasaba da karancin sinadarin iodine ta gudanar da taro domin nazarin hanyoyin kare jama’a daga cin karo da matsalar
Karancin sinadarin Iodine a jikin dan adam wani abu ne da masana suka gano cewa yana haifar da matsaloli da dama wa lafiyar dan adam.
Dalilin kenan da kungiyoyin irinsu asusun tallafin yara na majalisar dinkin duniya da Hukumar lafiya ta duniya WHO suka gargadi gwamnatoci akan bukatar daukar matakan hana amfani da gishirin girkin da ba ya kunshe da sinadarin Iodine ko iode a faransanci.
“Rashin gishiri mai dauke da iodine na kawo bari, ko a haifi yaro da karamin jiki ko ya shafi girmansa inda kwakwalwarsa ba za ta bunkasa kamar yadda ya kamata ba. Sannan ga rashin karfin jiki na yaro,” inji Dakta Fatima Sabo kwarariyar likita a fannin abinci mai gina jiki a asusun MDD mai kula da yara kanana UNICEF.
Bayanai sun yi nuni da cewa har yanzu matakan da gwamnatin kasar ta dauka ba su yi tasiri ba akan wannan matsala ta rashin amfani da sinadarin Iodine. Lamarin da yasa kwamitin kula da illolin karancin wannan sinadari a jikin dan adam ya shirya tattaunawa a tsakanin mambobinsa domin tsayar da shawarar da za ta taimakawa mahukunta bullo da dubarun shawo kan wannan matsalar.
Tsaurara matakan bincike akan iyakokin kasashe domin dakile barauniyar hanyar da ake shigo da gishiri maras sinadarin Iodine hade da karfafa bincike a kasuwanni domin tantance samfarin gishirin da ake saidawa mabukata na daga cikin abubuwan da aka yi imani a wurin wannan taro za su bada damar kare jama’a daga ilolin rashin cin abinci mai dauke da wannan sinadari.
Saurari rohoton Sule Mumin Barma
Facebook Forum