Duk da dadewar matsalar satar mutane don neman kudin fansa a wasu sassan Najeriya, wannan ne karon farko a arewa maso yammachin kasar da aka sace daruruwan dalibai maza a lokaci guda.
Dr. Yahuza Ahmed Getso, shi ne shugaban wata kungiyar al'umar arewachin Najeriya da ake kira Northern People Congress, ya na daga cikin masu jefa ayar tambaya game da yadda aka sace daliban makantar garin na Kankara, wadanda aka dawo da su daga baya, duba da cewa 'yar tazara ce ke tsakanin makarantar da wasu ofisoshin 'yan sanda da shingayen bincike a yankin.
Yanzu dai hankali ya karkata ne akan yadda za a lalubo mafita game da matsalar tsaro a Najeriya baki daya. Daya daga cikin masu sharhi kan al'amurran yau da kullum Kwamred Musa Zubairu Usman, ya ce ya kamata gwamnati ta duba kiraye-kirayen da jama'a ke yi akan nauyin da ya rataya a wuyanta, su kuma jama'a ya kamata su sanar da hukumomi duk wani abu da ya shafi tsaro da basu gane mai ba.
Akan batun neman mafita game da matsalar tsaron, Dr. Yahuza Ahmed Getso ya ce idan gwamnati da jami'an tsaro sun ce basu san inda masu kai irin wanna harin su ke ba, su sun san inda su ke kuma sun san yadda za a kamasu. Ya kara da cewa sun sha bada rahoto akan yadda makamai ke yawa da wadanda ke raba su a wurare amma sai su ga an sako mutanen daga baya.
Yanzu dai hauhawar hare-hare da sace mutane don neman kudin fansa sun sanya kungiyoyi da malaman addini da sauran shugabanin arewacin Najeriya maida hankali kan yadda za a magance matsalar tsaro a yankin baki daya.
Saurari rahoton Isah Lawal Ikara.