Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kano: Gunduje Ya Gana Da Manema Labaru Kan Bukukuwan Demokradiya Na Bana


Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje.

Da marecen jiya ne gwamnan na Kano ya yi wata ganawa da manema labaru a Kano kuma ya amsa wasu tambayoyi daga garesu.

Batun sha’anin tsaro, tarin basussukan ‘yan fansho, tura ma’aikatan gwamnatin ajujuwa domin koyarwa a makarantu da kuma aikin shimfida layin dogo na zamani na daga cikin manyan batutuwan da gwamnan Kano ya amsa tambayoyin manema labarai akan su, a wani bangare na bukukuwan demokaradiya na bana.

Dr Abdullahi Umar Ganduje ya fayyace dalilan da suka sanya ya nemi sansanin Jami’an tsaro a dajin Falgore na kudancin Kano.

Gwamnan ya kuma yi karin bayani game da manufar gwamnati ta mayar da ma’aikatan gwamnati su fiye da dubu biyar zuwa makarantun jihar domin su koyar.

A yayin zantawar, gwamnan na Kano ya yi bayani dai-dai gwargwado akan manufofi da aikace aikacen da gwamnatin sa tayi cikin shekaru 6 a bangarori daban daban na rayuwa.

Amma Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yi kokari matuka wajen kaucewa yin tsokaci akan kusan dukkanin batutuwan da suka shafi siyasa, kamar batun magajin sa a kujerar gwamna da mutumin da zai goyi baya a takarar shugaban kasa a 2023

Kalizaka, gwamnan ya ki yin bayani mai fadi akan sarkakiyar dake cikin asusun Fansho na jihar Kano da batun bada yancin kudi ga kananan hukumomi da bangaren shari’a da kuma majalisun dokokin na jihohi da sauran muhimman batutuwa.

Saurari cikakken rahoton a cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00

XS
SM
MD
LG