Hukumar da ke yaki da masu sayar da gurbatattun kayayyakin amfani ta KSCPC a Kano da ke arewacin Najeriya, ta lalata tan 402 na kayayyakin bogi da wadanda lokacin amfani da su ya wuce.
An kwace kayayyakin ne daga hannun ‘yan kasuwa a sassan jihar ta Kano, inda aka lalata su a ranar Lahadi.
Gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ne ya jagoranci aikin lalata kayan a harabar hukumar da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA reshen Kano.
Daga cikin kayayyakin da aka lalata kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, akwai magunguna, kayan abinci, kayan kwalliya, taba, hatsi da kuma kayan abincin dabbobi da na lemun kwalba.
A ‘yan kwanakin nan, jama’a a jihar ta Kano sun yi fama da mace-mace da rashin lafiya, sanadiyyar amfani da gurbatattu ko kayayyakin da lokacin amfani da su ya wuce.
A watan Maris akalla mutum uku suka mutu wasu daruruwa suka kwanta a asibiti bayan da suka yi amfani da wani sinadarin hada lemo wanda lokacin amfani da shi ya wuce.