Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Uber Zai Samar Da Motocin Sufuri Masu Tashi Sama


Kamfanin sufuri na yanar gizo “Uber” na gab da kammala shirye shiryen fara amfani da motocin sufuri masu tashi sama, yanzu haka kamfanin zai bude dakin gwaji “Laboratory” a turance a kasar Faris.

Kamfanin zai saka jarin kudi yuro milliyan ashirin kwatankwacin Naira billiyan goma, a cikin shekaru Biyar don samar da na’urori masu kula da shige da ficen motoci a lokacin da suke tafiya a cikin sararin sama.

Kamfanin ya bayyana cewar zai hada gwiwa da shahararriyar makarantar kerekere ta “Ecole” dake kasar ta Faransa, wannan wani yunkuri ne na shugaban kasar Faransa Macron, wanda yake kokarin ganin kasar ta taka muhimmiyar rawa a duniya a bangaren kimiyya da fasaha.

Kasancewar kasar Faransa na daya daga cikin kasashen da suka cigaba a bangaren kimiyyar jiragen sama, hakan zai taimaka wajen ganin anyi nasara a wajen fara amfani da wannan motar kasuwanci a kasar. Kamfanin Uber na sa ran fara amfani da motoci masu tashi sama a shekarar 2023.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG