Da safiyar yau ne gwamnatin kasar China ta kaddamar da wata na’urar “Satellite” a turance ita dai na’ura ce da zata rika kai rahotani tsakanin wannan duniyar zuwa sararin sama, a inda zata kwakwulo wasu bayanai da suke cikin duhu a duniyar wata.
Gidan jaridar kasar na Xinhua ya bayyana hakan, sun kara da cewar yau da misalign karfe 5:28 aka aika wannan nau’rar cikin wani kunbo mai suna March-4C daga tashar sadarwar binciken wata a yankin kudu maso yamma na kasar.
Wannan wani yunkuri ne da kasar ta China ke yi na ganin ta zama kasa ta farko da ta samo wasu bayanan yanayin duniyar wata zuwa duniyar yau, a cewar Mr. Zhang Lihua, shugaban hukumar binciken.
Ya kara da cewar na'urar taurarron dan’adam din zata isa duniyar ta wata bayan gudanar da tafiyar da ta kai kimanin kilomita dubu dari hudu da hamsin da biyar 455,000km, kuma wanna zai zama na’urar tauraron danadam ta farko a duniya da zata zauna a wannan mazauni.
Kasar ta China na kokarin ganin ta shiga sahun kasashe kamar su Rasha da Amurka a binciken duniyar wata nan da shekarun 2030. Kasar kuma na kokarin kaddamar da ofishinta mai zaman kanshi a duniyar ta wata a shekara mai zuwa.
Facebook Forum