Shugaban kamfanin Facebook Mark Zuckerberg, na cigaba da fuskantar tirjiya daga bangarori daban daban, tun a ‘yan watannin baya ne aka fara zargin kamfanin da hadin gwiwa da kasar Rasha, da yada kalaman kiyayya kana da amfanin da bayanan mutane, harma da daukar bayanai batare da izini ba.
Shugaban kamfanin ya gurfana a gaban ‘yan majalisun dokokin kasar Amurka, inda ya kare kamfanin na shi, yanzu kuma zai gurfana a gaban hukumomin kasashen Turai, inda zai amsa tambayoyi da suka shafi yadda kamfanin ke gudanar da aikin sa.
Kamfanin dai ya bayyana daukar karin ma'aikata 15,000 don ganin an kyautata yadda ake tsare bayanan jama’a batare da ba ‘yan kutse damar shiga asusun mutane ba, da kuma ganin an magance matsalar rubuce-rubuce marasa ma'ana, kamfanin zai kara yawan ma’aikata da zasu kai 20,000.
An kara jaddada cewar kamfanin na bukatar samar da karin ma’aikata da suka san dabi’u da al’adun kowane yanki, don ganin an samar da tsari da zai ba kowa damar bayyana ra’ayin batare da tsangwama ba.
Masana na ganin cewar ta haka ne kawai za’a ba mutane damar gabatar da rubuce rubuce da ba zasu take hakkin kowa ba, don haka kamfanin nada jan aiki wajen ganin an samar da yanayi da babu tsangwama ko wariya a yanar gizo.
Facebook Forum