Shugabar asusun bada lamuni na Duniya watau IMF tayi shawarwari da jami’an Najeriya, a fara ziyarar aikin ta na farko a Afirka.
Yau litinin ce shugabar asusun Christine Legard tayi shawarwari da shugaban Najeriya Goodluck Jonathan bayan ta gana da miistan kudi Ngozi Okonjo-Iweala a Abuja babban birnin Najeriya.
Kamfanin dillancin labaran najeriya ya ambaci shugabar tana cewa “ta gamsu sosai” da gaggawar da Mr. Jonathan yake son yin garambawul ga tattalin arzikin Najeriya, ya samar da ayyukan yi, d a kuma mai da hankali kan ayyukan noma.
Gobe Talata ake sa ran madam Legarde zata isa Legas domin wani taro kan makomar nahiyar.
Daga Najeriya shugabar asusun bada lamunin zata tashi zuwa Nijar inda zata gana da shugaba Muhammadu Isouffe, kuma ta shiga taron majalisar zartaswar kasar, wadda za a fi maida hankali kan kalubalen ci gaba ta fannin tattalin arziki da kasar take fuskanta.
Haka kuma zata yi jawabi ga majalisar dokokin Nijar, kuma zata gana da wakilan bankuna da ‘yan kasuwa masu zaman kansu.