Shugaban Kamaru Paul Biya shi ya karbi shugaba Francois Hollande a fillin saukar jiragen sama dake Yawunde babban birnin kasar.
Kamaru da Faransa suna da abun fadi. Wannan ziyarar zata ba shugaban Kamaru damar ambatar yakin da kasar ke yi da 'yan kungiyar ta'adanci ta Boko Haram da kuma irin taimakon da kasar Faransa take bayarwa ko kuma zata kara bayarwa nan gaba..
Wannan ziyarar dama ce ta tattaunawa akan dangantakar dake akwai tsakanin kasashen biyu wadda ta samu 'yar matsala a da can. Zasu kuma tattauna akan abubuwan da suka jibanci tattalin arziki, siyasa, al'adu da dai makamantansu.
Shugabannin zasu sa hannu akan yarjejeniyoyi hudu cikin ganawar awa daya da zasu yi. Daga bisani kuma akwai ganawa tsakanin bakon da 'yan majalisun kasashen biyu da kuma 'yan kasuwa.
Akwai kuma taron manema labarai da shugaban Faransan kafin cin abincin liyafa da yamma wadda mai masaukinsa ya shirya. Hollande zai gana da 'yan Faransa mazauna kasar Kamaru. Shugaban zai bar Kamaru da misalin karfe goma sha dayan dare komawa zuwa kasarsa.
Ga rahoton Manmadu Danda.