Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Tsaron Kan Iyakokin Kamaru da Najeriya na Taro a Yaounde


Sojojin Kamaru a Fotokol, Febrairu 17, 2015. (File Photo)
Sojojin Kamaru a Fotokol, Febrairu 17, 2015. (File Photo)

Taron, wata dama ce ta tantance irin matakan da ake dauka na yaki da 'yan ta'addan Boko Haram

Kwamitin tsaron kan iyakokin kasashen Kamaru da Najeriya na ci gaba da taro a birnin Yaounde. Kwamitin ya shiga kwana na biyu da fara tattaunawar ta kwanaki uku.

Kwamitin tsaron kan iyakokin kasashen biyu na yin taron ne da nufin wanzar da zaman lafiya a kan iyakokin su, da kuma kawo karshen tashe-tashen hankulan da 'yan kungiyar Boko Haram ke haddasawa akai-akai.

Karo na uku kenan da kwamitin kan iyakokin Kamaru da Najeriya ke shirya irin wannan taro.

A ranakun takwas zuwa goma sha daya ga watan yulin shekarar da ta gabata ta dubu biyu da goma sha hudu kwamitin yayi taron shi na biyu a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

Wakilin Sashen Hausa a kasar Kamaru Mamadou Danda ya aiko karin bayani akan taron kamar haka:

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:43 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG