Mataimakiyar Shugaban Amurka Kamala Harris za ta yi hira da gidan talabijin na CNN.
Wannan shi ne karo na farko da Harris za ta zanta da wata kafar yada labarai tun bayan da Shugaba Joe Biden ya janye takararsa ya nuna mata goyon baya.
Za a nuna hirar a ranar Alhamis da misalign karfe tara agogon yankin gabashin Amurka.
Abokin takararta Gwamnan jihar Minnesota Tim Walz zai kasance tare da ita a lokacin hirar wacce za a yi a Georgia.
An jima ana caccakar Harris da kin taron manema labarai ko a yi hira da ita tun da ta kaddamar da yakin neman zabenta a ranar 21 ga watan Yuli.
Hakan ya budewa ‘yan Republican kofar caccakarta inda suke nuni da kin yin hira da kowa.
Mai yiwuwa, wannan hirar ta ba Harris damar kwantar da kurar da ke tashi kan kin ganawa da manema labarai, a gefe guda kuma ta kan iya zama tattare da kasada yayin take kokarin tsayawa da kafarta tun bayan sauyin dan takarar da jam’iyyar ta Democrat ta yi.
Dandalin Mu Tattauna