Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harris, Trump Na Rige-rigen Tara Kudaden Yakin Neman Zabe


Zaben Amurka: Kamala Harris, hagu, Donald Trump, dama
Zaben Amurka: Kamala Harris, hagu, Donald Trump, dama

Mataimakiyar Shugaban kasa Kamala Harris ta ce yakin neman zabenta ya tara dala miliyan 540 ya zuwa yanzu kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito.

Hakan na nufin ta dara abin da tsohon Shugaban kasa Donald Trump ya tara.

Tun bayan da Shugaba Joe Biden ya janye takararsa ya kuma nuna goyon baya ga Harris, yakin neman zabenta ya ga karuwar masu ba da gudunmowa.

Gangamin yakin neman zaben nata har ila yau ya ce ya ga karuwar masu ba da tallafin a lokacin babban taron jam’iyyar Democrat da aka yi Chicago a makon da ya gabata inda Harris da dan takarar mataimakin shugaban kasa Tim Walz suka amince da zabin da aka yi musu.

Shi ma dai Trump ba a bar shi a baya ba wajen tara kudaden, domin a farkon watannan na Agusta ya sanar da tara dala miliyan 138.7 a cikin watan Yuli kadai.

Hakan ya yi kasa da abin da yakin neman zaben Harris ya tara a makon farko da ta kaddamar da yakin neman zabenta.

Yakin neman zaben Trump a halin yanzu ya ce yana da jimullar ruwan kudi dala miliyan 327 tun daga farkon watan Agusta.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG