Paul Ryan kakakin majalisar dokokin Amurka wanda yake rike da mukami mafi girma a cikin 'yan Republican ya fada jiya Alhamis cewa shi bai shirya ba Donald Trump goyon baya ba.
Tun farko Paul Ryan ya soki Donald Trump lokacin da yace idan ba'a tsayar dashi dan takarar jam'iyyar ba magoya bayansa zasu yi bori a taron koli na jam'iyyar ita Republican da za'a yi a watan Yuli.
Ryan yace "ina fata zan iya goyon bayan wanda muka tsayar. Ina fata zan iya bashi cikakken goyon baya. Amma adaidai wannan lokacin ban shirya ba, inji Ryan.
Mujallar Wall Street ta wallafa a wani shafinta cewa 'yan majalisu 12 kacal cikin 300 na 'yan Republican suka ba attajirin goyon bayansu. Haka ma gwamnoni uku kawai cikin 31 suka nuna suna goyon bayan attajirin.
Tsoffin shugabannin Amurka biyu dukansu 'yan Republican sun ce zasu kauracewa taron kolin jam'iyyar kuma sun sha alwashin ba zasu bude bakinsu su ce komi ba.
Haka ma tsoffin 'yan takaraan shugabancin kasar, John McCain wanda ya kara da Barack Obama a shekarar 2008 da Mitt Romney da shi ma ya fafata da Obama a shekarar 2012 sun ce zasu kauracewa taron kolin watan Yuli inda ala tilas jam'iyyar ta tsayar da Donald Trump.