Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kaikaiyi Ya Koma Kan Mashekiya, Ga Wasu 'Yan Harin Kunar Baki Wake


Barnar 'yan Boko Haram.
Barnar 'yan Boko Haram.

Yan sanda a arewa maso gabashin Nigeria sunce wasu mata masu harin kunar bakin wake a yau Asabar kaikayi ya koma kan mashekiya, a lokacinda bam din dake makele da jikinsu ya tashi ya kashe su a lokacinda suke kokarin samun motar da zata kai su birnin Maiduguri.

Yan sanda a arewa maso gabashin Nigeria sunce wasu mata masu harin kunar bakin wake a yau Asabar kaikayi ya koma kan mashekiya, a lokacinda bam din dake makele da jikinsu ya tashi ya kashe su, suna kokarin samun motar da zata kai su birnin Maiduguri.

Wani jami'in 'yan Sanda ya fadawa Muryar Amirka cewa matan suna tsaye a gefen hanya kuma suna kokarin samun motar da zata kai su Maiduguri a Jakana, kimamin kilomita arba'in yamma da birnin Maiduguri. To amma cikin ikon Allah duk motar da suka yi kokarin tsayarwa, tayi watsi dasu.

Yace da misali karfe hudu da mintoci ashiri na la'asar sai yan sanda suka ji karar fashewa. Yace da suka je inda fashewar ta auku, sai suka iske gawar dayan mace bam yayi kaca kaca da ita, ita kuma dayar ta mutu, da damarar bam a jikinta

Yace sai sa 'yan sanda suka jira masa masu kwance bam, kafin suka kwashe gawarwarkin matan.

Jami'in na yan sanda yace yanzu direbobi a Maiduguri da kewayen birni Maiduguri suna tsoron taimakon matan dake tsaye a gefen hanya, a saboda abubuwan da suka fara a baya domin yanzu harda da mata cikin 'yan harin kunar bakin wake.

A ranar Litiinin data shige mata wata mace yar hari kunar bakin wake ne ta tarwatsa kanta a kasuwar Baga inda ake sayar da kifi ta kashe akalla mutane talatin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:31 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG