Mataimakin gwamnan jihar Borno Alhaji Zannan Umar Mustapha y ace gwamnatin da ta shude ba ta mata adalci ba game da matsalar Boko Haram da ta shafe shekaru sama da hudu ta na fama da ita. Da yak e karbar kayan tallafi daga wurin hukumar hana fasakwabri ta ‘CUSTOM,’ Alhaji Mustapha y ace a maimakon a dau matakan da su ka dace kan Boko Haram sai kawai aka maida al’amarin wata harkar siyasa; kuma duka-duka abin da gwamnatin taryyar Najeriya ta bas u shi ne Naira miliyan 200.
Y ace kananan hukumomi 22 na jihar Borno sun fada hannun Boko Haram lokacin da aka bas u naira miliyan 200 kawai; amma da kananan hukumomin jihar Adamawa biyar zuwa shida su ka fada hannun Boko Haram, sai aka ba ta naira biliyan hudu. Y ace babu irin wahalar da bas u sha ba a jihar Borno; hasalima, kusan dukkannin kananan hukumomin sun gudu sun tare a birnin Maiduguri, inda a yanzu haka ake da sansanonin ‘yan gudun hijira har 22. Y ace kusan watanni 6 kenan da rufe makarantu a jihar ta Borno kuma ana amfani da su a matsayin sansanonin ‘yan gudun hijira.
Mataimakin gwamnan, wanda ya jinjina ma hukumar ta kwastam, y ace jihar Borno ta kashe naira biliyan 11 wajen kula da ‘yan gudun hijirar. Shi kuwa Alhaji Tahir Musa Mataimakin Kwantarola-Janar na kasa kuma wanda ya wakilci Alhaji Abdullahi Dikko Inde Shugaban hukumar Kwastam na kasa, y ace ba daga asusun gwamnati aka tara gudunmowar ba, kuma ba daga irin kayakin da su kan kama ba ne, karo-karo ma’aikatar hukumar ta kwastam su ka yi bisa umurnin Shugaban hukumar na kasa.
Alhaji Musa y ace cikin abubuwa wajen 70 da su ka kawo akwai shinkafa da madara da indomi da tukwanen dahuwa da tufafi da takalma da tabarmu da dai sauransu. Y ace a baya ma sun ba da shinkafa wajen buhu 100,000, wato tireloli sama da 200.