A daidai lokacin da masu ruwa da tsaki a batutuwan da suka shafi makomar Najeriya ke ci gaba da tattaunawa akan batun dagewa ko jinkirta zabe, ita dai hukumar zaben kasar mai zaman kan ta, INEC a takaice, ta dage cewa babu dalilin dage zabe ko jinkirta shi domin a shirye ta ke.
Sai dai kuma duk da cewa hukumar zabe, INEC, ta ce a shirye ta ke ta gudanar da zabe a ranar goma sha hudu ga watan Fabarairu, masu goyon bayan a yi zaben, da wadanda ke ganin cewa a jinkirta, su na ci gaba da bayyana ra'ayoyin su da suka sha bamban.
Su dai 'yan babbar jam'iyar hamayyar kasar Najeriya APC su na goyon bayan cewa a yi zabe a ranar goma sha hudu ga watan Fabrairu kamar yadda aka tsaida, a yayin da bangaren jam'iyar PDP mai mulkin kasar kuma ke bayyana ra'ayin dake nuna cewa ba sa so a yi zaben yanzu.
Kamar yadda ku ka ji a karshen rahoton wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka Nasiru Adamu el Hikaya ne ya aiko shi daga Abuja.